Wayar Da Kan Mata Da Iliminsu Shine Burin Mu

Maryam Tafida Bello Shugaban Girls Rising

Shirin da “Bazarmu” shirin ne na wayar da kan al’umar duniya akan muhimmanci ilimin ‘ya'ya mata da kuma koya musu sana’oin dogaro da kai ta yadda zasu taimakawa kansu da ‘ya’yansu da kuma al’umominsu.

Shugabar kungiyar girls rising, a nan Nigeria, Maryam Tafida Bello, ce ta bayyana haka a wani taron karawa juna sanin na yan jaridu, ta ce shirin zai dinga nuni ne da wasu muhimman mata da zasu rika fitowa cikin fina-finan da kungiyar ta Girls Rising, ta shirya da wasu matan arewa su 6, daga cikin mata 12 da ta shirya a duniya a wani gidan talabijin.

Su dai wadannan mata na bada labarinsu ne da yadda rayuwarsu ta kasance tun daga farko har zuwa ga yadda suka cimma burikansu na kokarinsu na tabbatar da cewa sun nemi ilimi.

Hajia Maryam ta ce tana fatan 'yan jarida zasu dora a inda kungiyarta ta tsaya don bunkasa ilimin ‘ya’ya mata, a cewar ta kungiyar Girls Rising, ta fara, kuma ragowar ta rage ga alummar gari su dora akan shinfidar da kungiyar ta Girls Rising tayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Wayar Da Kan Mata Da Iliminsu Shine Burin Mu - 4'54"