Kamar yadda muka saba tattaunawa da samari da 'yan mata a kowane karshen mako domin jin ra'ayoyinsu akan batutuwa daban daban da suka shafi rayuwa, soyayya da zamantakewa da sauransu, shirin samartaka na wannan makon ya mayar da hankali ne a kan amfani da wayar hannu ta hanyoyin da basu dace ba.
Matasa maza da mata na amfani da wayar hannu ta hanyoyin da basu dace ba kamar aikawa juna hotuna da bidiyo da suka sabawa addini da al'ada, da kuma daukar lokaci mai tsawo una tattaunawa da juna cikin tsakiyar dare wato Free call, wanda yawanci yakan kai ga aikata abubuwan da basu dace ba.
Da dama sun bayyana ra'ayoyinsu da kuma irin nasu tunani dangane da wannan lamari, har ma da irin nasu dalilan na ganin cewa hakan bashi da wani aibi.
Domin karin bayai, saurari cikakkiyra hirarn a nan
Your browser doesn’t support HTML5