Galibi kasashen duniya sun goyi bayan takunkunmi baya bayan nan da aka azawa kasar Korea ta kudu, to amma akwai da yawa da suke tababan ko takunkunmin zai yi wani tasirin azo a gani kuwa.
Jiya Litinin bai daya kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince a azawa Korea ta arewa takunkunmi tattalin arziki mai gauni a saboda gwajin makami nukiliya da ta yi a ranar uku ga wannan wata na Satumba.
Jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta fada jiya Litini da maraice cewa, yau kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana fadawa gwamnatin Korea ta arewa cewa idan bata kawo karshen shirin ta na nukiliya ba, to kwamitin zai dauki matakin dakatar da ita.
Idan dai aka kaddamar da sabbin takunkunmin yadda ya kamata, to zasu ragewa Korea ta arewa hanyoyin samun kudaden kasashen waje da take bukata.