Wata ‘Yar Sudan Ta Kudu, Rita Lopidia Abraham, Ta Samu Lambar Yabon Samar Da Zaman Lafiya

Rita Lopidia Abraham (Courtesy EVE)

A Sudan Ta Kudu, wata gallabi tsakanin rawwuna a fagen kawo zaman lafiya, ta samu lambar yabo ta rukunin mata. Wannan ya biyo dagewar da ta yi wajen wanzar da zaman lafiya

Yar rajin gwagwarmayar samar da zaman lafiya ta Sudan ta Kudu, Rita Lopidia Abraham ta samu lambar yabon samar da zaman lafiya ta mata ta shekarar 2020 a jiya Talata daga cibiyar samar da zaman lafiya ta Amurka da ke Washington.

Rita ta fada wa shirin South Sudan in Focus na Muryar Amurka cewa gwagwarmayarta ta samar da zaman lafiya a Sudan ta kudu jan aiki ne mai cike da barazana daga mazan da ke kan teburin shawarwari.

“Wani lokacin idan ka yi magana da bangarorin biyu kuma ka fada wa hukumomi gaskiya, mutane basa fahimtarka,” a cewarta. Abin takaici ne saboda babban burin shi ne samar da zaman lafiya a karshe. Amma ba haka lamarin ya ke ba da bangarorin Sudan Ta Kudu da ke fada.

Za a ba Rita kudi dala 10,000 da zata yi amfani da su a duk lokacin da ta so kuma cibiyar zata karrama ta a wani biki da za a yi a shekarar 2021