Taron wasu masana kimiyya a kasar Australia, ya nuna cewa an kirkiri wata na’ura mai tunanin kanta wajen samar da maganin mura.
Masanan da suka fito daga jami’ar Flinders, na da yakinin cewar wannan shi ne karon farko da aka taba amfani da na’ura mai tunanin kanta a fadin duniya wajen kirkirar magunguna don amfanin mutane.
Na’urar mai kwakwalwa da aka sama suna "Sam ko Search Algorithm for Lingands" wata sabuwar fasaha ce da na’urar ke tunanin adadin sinadarin da ake bukata, wajen samar da maganin da ke kauda cutar mura da ma wasu cututtuka da ake kamuwa da su a sanadiyyar cudanya da mutane.
Abin da kawai na’urar ke bukata shi ne a saka mata nau’ukan magungunan da ake da su, wadanda suke aiki da wadanda ba su yi a jikin dan’adam, sauran kuma ya rage gareta ta fito da sabon magani daidai da tunaninta da zai yi aiki a jikin bil’adama, ba tare da taimakon kowa ba.
Masanan sun kira wannan sabon tsarin da cewar shi ne binciken “karni na 21” a cewar Dr. Nikolai Petrovsky, mun yi amfani da nau’ukan magunguna 2, da wanda ke aiki da wanda ba su aiki muka saka ma na’urar sai ta tantance sabuwar hanya da samar da sabon magani bisa iya tunaninta.
Ya kuma kara da cewar, mun gwada magungunan da ta yi kuma sun yi aiki kwarai da gaske a jikin bil'adama.