Wata Sabuwar Hanya Da Boko Haram Ke Jan Hankalin Matasa

Yan Matan Chibok

Hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar da wata sanarwa dake ankarar da jama’a kan yadda ‘yan ta’addar Najeria ke jan hankalin matasa ta hanyar basu lamani, kuma wannan tsari na gudana ne musamman a Arewa maso Gabas.

Kakakin rundunar tsaron Najeriya Birgediya Janal Rabe Abubakar, yace lamanin na tunkarar Mahauta da Tailoli da sauran masu sana’ar hannu don su fada aikin Boko Haram.

Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya, ya tuntubi kwararre kan fannin ta’addanci Dakta Mohammad Bello na jimi’ar Jigawa, wanda yace ana yaudarar matasa da kudi a matsayin jari amma ba biya zasuyi ba, ana hakane domin ayi dabarar janyosu jiki a tura musu mummunan akida.

Kamar yadda shedun gani da ido ke cewa a baya ‘yan Boko Haram, kan tilastawa maza musamman ma matasa shiga kungiyar idan sunki kuwa su fuskanci kisa, su kuwa mata ana awan gaba ne dasu. Koma dai ta wacce hanya Boko Haram ke samun mayakanta, a zahiri dubban rayuka sun salwanta, garuruwa sun zama kango, masiface mai muni tun bayan mai Tatsine.

Saurari rahotan El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Sabuwar Hanya Da Boko Haram Ke Jan Hankalin Matasa - 2'56"