Wannan sabon rikicin ya taso ne bayan da wata babbar kotun jihar Ribas ta dakatar da shugaban jam’iyyar ta PDP na kasa Prince Uche Secondus daga mukaminsa, a daidai lokacin da kuma dukan masu fada a ji suke kokarin hada kai domin magance wata takaddama da ke kokarin farraka jam’iyyar.
Bayan dakatar da Secondus da kotu ta yi, sai mataimakan shugaban jam’iyyar biyu, na yankin kudu Yemi Akinwonmi, da na yankin Arewa Suleiman Nazif, kowannensu ya fitar da sanarwa cewa shi ne halataccen mukaddashin shugaban jam’iyyar.
Akinwonmi dai ya kafa hujja da sashe na 35 (3)(b) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta PDP, wanda ya ce shi ne ya ba shi ikon kasancewa mukaddashin shugaba a lokacin da babu shugaban na kasa.
Kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta PDP dai ya yi tanadin cewa “Idan aka sami daya daga cikin rashin shugaba na kasa ta hanyar murabus, cirewa, mutuwa ko kasa iya gudanar da aiki, to mataimakin shugaba daga yankin da shugaban ya fito ne zai dare mukamin a zaman mukaddashin shugaba.”
To sai dai a na shi bangare kuma, Nazif ya kafa hujja da aya ta gaba ta kundin tsarin mulkin, inda ya ce “Idan kuma aka sami rashin shugaba da mataimakinsa daga yankin da shugaban ya fito, to sai mataimakin shugaba daga daya yankin ya haye mukamin mukaddashin shugaban jam’iyyar.”
A kan haka ne Nazif ya ba da sanarwar cewa "daya mataimakin shugaban jam’iyyar daga yankin kudu da ya kamata ya kasance mukaddashin shugaba, ta bayyana cewa ba zai iya gudanar da aiki ba. Hasali ma ba ya halartar tarukan shugabannin jam’iyyar na kasa tsawon watanni 9."
Nazif ya kara da cewa tun da ko babu wancan, to shi ne halataccen mukaddashin shugaban jam’iyyar.
Nazifi ne na farko da ya garzaya shelkwatar jam’iyyar ta kasa jim kadan bayan umarnin kotu na dakatar da Secondus, inda kuma ya gudanar da wani taro na tabbatar da cewa shi ne mukaddashin shugaba.
To sai dai kuma sa’o’i 3 bayan taron, sai shi kuma Akinwonmi ya garzaya da tashi tawagar, ya kuma yi nashi taron da ke wargaza dukkan abin da aka yi a taron farko na Nazif.
Jam’iyyar ta PDP dai ta jima tana fama da baraka wadda ta samo asali daga shugabanci, da kuma shirye-shiryen babban zaben shekara ta 2023 mai zuwa.
Sau da dama kuma ana gudanar da taruka na masu ruwa da tsaki domin samo bakin zaren warware wannan takadda, lamarin da har kawo yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Kafin samun wannan umarnin na kotu, Uche Secondus ya yi kememe cewa ba zai sauka daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar ba har sai wa’adinsa ya kare a watan Disamban wannan shekara, duk kuwa da cewa taron na sulhu, ya yi matsayar shirya babban taron jam’iyyar kafin wannan lokacin.