Wata Mota Kirar Tesla Mai Tuka Kanta Ta Tunkuyi Wata Motar 'Yansanda

Wata mota kirar Tesla mai tuka kanta ta tunkuyi wata motar ‘yan sanda a gefen wani babban titi a jahar Connecticut, yayin da ‘yansanda su ke cikin aikace-aikacensu na yau da kullum.

Kafin wannan hatsarin, 'yansanda ne kawai su ka je wurin don duba wata mota da ta lalace a hanyar, amma sai kawai wurin ya hargitse bayan da mota kirar Tesla din ta tunkuyi motar 'yansandan da ke gefen titin da farko, sannan ta kuma tunkuyi motar da ta lalace din sannan daga bisani dai ta tsaya tare da taimakon wani dansanda.

Direban ya fada wa ‘yansanda cewa ya na kan leka karensa kenan da ke zaune a bayan kujera yayin da ya mai da motar a tsarin tuka kanta na Autopilot. Tesla dai ba ta tallata Autopilot a zaman tsarin mota mai tuka kanta ba gaba daya, koda shike sunan dai har yanzu ya kasance mai cike da takaddama, kuma masu suka suna cewa ya fi ƙarfin ikonta. Tesla dai ba ta bada amsar bukatar neman bayani ba game da wannan lamarin.

"A cewar Hukumar Kula da zirga-zirgar motoci na kasa, kodayake motoci da yawa na da tsarin sarrafa kansu, babu wasu motocin da ake sayarwa a halin yanzu masu sarrafa kansu ko kuma tuka kansu." In ji sanarwar. Sanarwar ta kara da cewa, "duk da cewa, motar ka na da damar sarrafa kanta, a duk lokacin da ka ke tuka abin hawa, ana buƙatar cikakkiyar kulawa da sa ido a ko da yaushe don tabbatar da tuki lafiya lau."