Wata Mata Ta Auri Mazaje Takwas a Amurka

file photo

Wata kotu a birnin New York dake Amurka ta tuhumi wata mata da auren maza takwas a cikin lokacin guda amma kuma matar tace sam bata yi laifi ba.

Aranar juma ne dai wata kotu dake ‘kauyen Broxnville ta gurfanar da matar akan laifuffuka biyu a kokarin ta na samun takardan zama yar kasa.

Ita dai wannan baiwar ALLAH mai suna Liana Barrientor yar shekaru 39 ta auri mutane daga kasashe dabam dabam da suka hada da Masar, Turkiyya, da Geogia dake nan kasar Amurka da dai sauran kasashen duniya, wani dan kasar Pakistan ne mutum na takwas data aura mai suna Rashid Rajput, kamar yadda mai gabatar da kara a lardin na Bronx ya fada.

Sai dai an tasa keyar Rajput zuwa kasar sa a shekarar 2006 biyo bayan binciken da aka yi game dashi na kalaman barazana ga kasar ta Amurka, kuma hukumar sha yanzu magani yanzu ce wato hukumar shige da fice ta yi hakan.

Wannan hukumar wadda wata bangare ce ta ma’aikatar tsaron cikin gida ta danganta wasu kasashe dake da jan tuta a matsayin masu kokarin shigowa kasar ta Amurka da wasu abubuwan da basu dace ba.

Sai dai matar mai maza takwas, mai suna Barrientor, tace ita fa bata yi laifi ba a lokacin da mai sharia ke tambarta, bayan anga zoben shaidar cewa tana da aure a hannun ta.