Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Talemsi a jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijer ta taimakawa matasar jiha da kayan aiki da jari da ya kai miliyon ashirin da daya na CFA don kara musu kwarin gwiwa yin sana’a a gida.
Shugaban Kungiyar Talemsi mai zaman kanta yace kungiyar ta dauki wannan mataki ne ganin yanda matasa ke bin barauniyar hanya zuwa kasashen Turai wasu kuma suna bada kansu ga masu safarar bil adama, kana wannan taimako zai sa matasan su dogara ga sana’o’insu.
Shugaban na kungiyar yace an baiwa matasan zabi ne su nuna abubuwa da suke bukata da zasu yi sana’a da su. Bayan ya mika godaiya ga wadanda suka tallafawa wannan shiri ya yi kira ga matasan cewar a cikin gida aka basu wannan taimako don haka su yi amfani da kayan aikin a cikin gida.
Irin wannan taimako na cikin gudunmuwa da kungiyoyi masu zaman kansu a jamhuriyar Nijer ke yi ga yaki da safarar mutane. Sanusi Mahaman mamba ne kungiyar farar hula ya yi kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan taimako da Talemsi ta baiwa matasa.
Your browser doesn’t support HTML5