Wata kungiyar tsagera dake da’awar Musulunci ta dauki alhakin harin boma bomai da wani hari a ajiberen Kirsimeti

Wadansu da suke jinyar raunuka da suka samu a harim boma bomai da aka kai birnin Jos a jajibirin Kirsimati.

Wata kungiyar tsagera dake da’awar Musulunci ta dauki alhakin harin boma bomai da wani hari kan wata majami’a a jajiberen kirsimeti da ya yi sanadin mutuwar mutane 86.

Wata kungiyar tsagera dake da’awar Musulunci ta dauki alhakin harin boma bomai da wani hari kan wata majami’a a jajiberen kirsimeti da ya halaka akalla mutane tamanin da shida. Kungiyar Boko Harama ta fada jiya Talata cewa zata ci gaba da kai hare haren kan abinda ta kira mutane da basu yi imani ba. Jami’ai a Najeriya sunce akalla mutane tamanin ne harin da aka auna kan kiristoci a birnin Jos dake cefenen karshe kamin kirsimeti ranar jumma’a da ta shige. A ranarr ce kuma aka kaiwa wasu majami’u da dama hari a birnin Maiduguri aka kashe mutane akalla shida.