Wata Hadakar Kungiyoyin Jahar Taraba Ta Nemi Gwamna Darius Ya Gayawa Duniya Wadanda Suke shirin Kawo Hari A Jahar.

TARABA: Gwamna Darius Dickson

Biyo bayan kalaman da gwamnan jihar Taraba,Darius Dickson Isiyaku yayi na cewa za’a kawo jihar hari nan da kwanaki goma, yanzu haka yan jihar sun soma maida martani tare da yin kira da a gaggauta gudanar da bincike.

Shi dai gwamnan wanda ya zargi gwamnatin tarayya da shakulatin bangaro game da abubuwan dake faruwa,yace dole jihohi su dauki matakin kare kai.

Gwamnan wanda ke yiwa tawagar shugabanin jam’iyar PDP ta kasa da suka ziyarce shi a Jalingo,yace su yanzu suna cikin mawuyacin hali,kasan cewar basa iko da jami’an tsaro.

‘’ Yanzu ina zaune ne tamkar sarkin da babu rawani akai, domin baka iko da yan sanda ko jami’an tsaro,duk lokacin da muka nemi dauki ba’a kawo mana da gaggawa,wai sai sun sami umarni daga Abuja.

‘’Yanzu haka ana shirin kawo mana hari nan da kwanaki goma,kuma kwanannan wani jirgin sama mai saukar angulu wato ya sauka a wani kauye cike da makamai, dole mu fadawa duniya halin da muke ciki,’’ a cewar gwamnan jihar Taraban.

Yanzu haka ma dai, wannnan kalaman gwamnan ya tada hankulan jama’an jihar inda wasu kungiyoyi ke kira ga gwamnatin Najeriya data hanzarta binciken wannan lamari.A wajen wani taron manema labarai da hadakar kungiyar cigaban Taraba,ta Taraba Concern Citizen Forum ‘’ ta kira a Jalingo,shugaban kungiyar Barr.M.B Mustapha ya bayyana kalaman gwamnan da katobara da ya kamata a bincika.

To sai dai kuma hukumomin tsaro a jihar sun ce,kawo yanzu basu sami bayanan da gwamnan ke zargi ba,kuma su kullum a shirye suke na dakile duk wani hari,ko fitina da ka iya tashi a jihar.ASP David Misal,kakakin rundunan yan sandan jihar Taraban,ya bukaci jama’a da su bada bayanan duk wani abu da basu amince da shi ba.

Hakanan kuma kakakin yan sandan ya musanta zargin da gwamnatin jihar ta yi na cewa Fulani makiyaya sun kashe wasu tibabe hudu a yankin Gassol.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamna Darius kan hari da za'a kawo jahar.

File: