Ma'aikatar shari'ar kasar Najeriya ta shirya tsaf ta gurfanar da Dr. Bukola Saraki shugaban majalisar dattawa gaban wani kotu yau Juma'a.
Ma'aikatar ta tsara tuhume tuhume har guda goma sha uku akan shi Dr Bukola Saraki da zata gabatar yau. To amma kwatsam sai wata kotun tarayya dake karkashin mai shari'a Ahmed Muhammad ta dakatar da gurfanar da shugaban majalisar gaban kotu har sai ta saurari karar da aka shigar gabanta.
Kotun tarayyar ta gayyato ma'aikatar shari'a da shugaban hukumar da'a ta kasa da shugaban kotun da aka shirya gurfanar dashi Bukola Saraki duka su bayyana a gabanta ranar 21 ga wannan watan domin su bayyana mata dalilan da suka sa za'a gurfanar da Dr. Bukola Saraki gaban kotun.
Kazalika a cikin wadanda aka gayyato sun hada ma da wani mataimakin darakta a ofishin atoni janar na tarayya Mr. Muslim Hassan.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5