Wata Kotun Faransa Ta Bukaci Tsohon Shugaban Kasa Sarkozy Ya Bayyana Gabanta

Tsohon shugaban Faransa Nocolas Sarkozy da marigayi shugaban Libya Ghadafi

Tsohon shugaban Faransa Nocolas Sarkozy da marigayi shugaban Libya Ghadafi

Watan gobe ne tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy zai gurfana gaban kotu bisa zargin cin hanci da rashawa tare da karban tallafin kudi daga marigayi shugaban Libya Moammar Ghadafi shekaru 11 da suka gabata

Jiya Alhamis ne wata Kotun Faransa ta umarci tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy ya gurfana gabanta bisa zargin cin hanci da rashawa da amfani da martabarsa ta hanyoyin da basu dace ba.


Shari’ar zata mai da hankali ne a kan magana ta wayar tarho da ake zargin Sarkozy ya yi da wani alkali dake binciken zargin yakin neman zaben Sarkozyn a shekarar 2007, ya sami gudumawa ta barauniyar hanya.


Ana zargin dan siyasar mai ra’ayin mazan jiyan ne, yayi alkawarinn zai sa a karawa alkali mai bincikensa girma, idan ya amince zai bashi wasu muhimman bayanai game da binciken yakin neman zaben sa. A wannan magana da alkali Gilbert Azibert, babban alkali a babbar kotun kasar, Sarkozy ya ce zai taimaka ya bashi wani babban mukami a Monaco mai makwabta da Paris. Yan sanda sun dauki hirar da suka yi akan fei-fei.


Sabbin bayanai da aka samu suna zuwa ne, kwanaki bayan da aka kaddamar da bincike a kan ikirarin cewa Sarkozy ya karbi tallafin kudi daga hannun marigayi tsohon shugaban Libya Moammar Gadhafi, da ya kai shi ga lashe zaben shugaban kasar shekaru 11 da suka wuce.

Sarkozy ya musunta aikata laifi, kana lauyoyinsa sun ce zasu daukaka kara a kan shawarar gurfanar da shi gaban shari'a, a wani zaman kotu da za'a yi a ranar 25 ga watan Yuni.


Haka ma an bukaci Lauyan Sarkozy, Thierry Herzog, da alkali Azibert, su ma a gurfanar da su.