Wata Kotun Majistare a karamar hukumar Westminster kasar Ingila, ta yanke wa mai tsaron raga na kasar faransa, wanda ya jagoranci tawagar kasar faransa a matsayin Kaftin, a gasar cin kofin duniya 2018, har ta lashe gasar kuma mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Tottenham mai suna Hugo Lloris, hukuncin haramta masa tuki har na tsawon watanni 20, tare da biyan tarar fan kudi dubu £50,000 kudin Ingila sakamakon samunsa da laifin yin tuki cikin maye.
Dan sanda mai gabatar da karar Henry Fitch, ya ce an kama Hugo Lloris ya zarta a guje da motarsa har ta wuce motocin dake tsaye a yayin da aka tsayar da su, kafin ya lura ya gyara dan haka bincike ya nuna cewa ya sha barasa fiye da kima.
Hakan ya sabawa dokar kasar, don hakannema aka gurfanar dashi a gaban kuto, kuma wannan ba shine karo na farko da aka taba samunsa da irin wannan laifi ba. Lokacin da aka yanke hukunci, alkalin kotun ya ce ya yi hakanne duba da muhimmancin laifin da kuma matsayin wanda ya aikata shi, Hugo Lloris ya amsa wannan laifi da ake tuhumarsa dashi.
Wakilin dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba yayi alkawarin dan wasan zai tafi zuwa kungiyar Barcelona ko Real Madrid a karshen wannan kakar.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, na cikin hatsarin rasa dan wasanta Cesc Fabregas, mai shekaru 31 da haihuwa, inda ake ganin zai koma kungiyar
Inter Milan ko AC Milan a watan Janairu, bayan da kwantirakin dan wasan tsakiya na Spain zai kare a Stamford Bridge karshen kakar wasa ta bana.
Dan wasan Manchester City, David Silva, mai shekaru 32, a duniya yana so ya koma Las Palmas ta Spain a lokacin da kwangilarsa ta kare a shekarar 2020 kuma nanne mahaifarsa a Gran Canaria.
Your browser doesn’t support HTML5