Alkali Adedayo Oyebanji shi ya yanke hukuncin bayan da wani dan kasuwa mai suna Dr. Emmanuel Fijabi Adebo tare da kamfaninsa Fijabi Adebo Holdings Limited suka kai karar kamfanin COKACOLA da kuma NAFDAC.
Kotun ta yanke hukumcin cewa shan lemunan suna da illa ga bil'Adama. Ta bukaci hukumar NAFDAC ta biya wadanda suka shigar da karar. tarar N2m.
Acewar kotun hukumar NAFDAC tayi sakaci na kin shaidawa 'yan Najeriya cewa akwai lahani tattare da shan lemun na Sprite ko Fanta.
Lauyan da ya shigar da karar Mr Abiodun Oni Dare yace a watan Maris na shekara da 2007 kamfanin Fijabi ya sayi Cokacola da Fanta da Sprite da dai wasunsu domin kaiwa kasar Birtaniya. Amma bayan da kayan suka isa Birtaniya sai hukumomin lafiya na kasar suka kwace kayan saboda lemun suna da lahani ga bil'Adama.
Yayinda yake kare kamfanin COKACOLA lauyansa Mr. T.O. Busari yace lemunan da ake magana a kai an yisu ne domin sha a Najeriya ba wai a kaisu kasashen waje ba. Saboda haka, injishi lemunan ba haramtattu ba ne a cikin Najeriya.
Wannan kariyar da lauyan ya bayar ta kara nuna sakacin hukumar NAFDAC akan abubuwan da 'yan Najeriya ke ci ko sha saboda rashin sa ido sosai.
Yawancin masu shan lemun basu san yawan vitamin C dake cikin lemun da suke sha ba. Wani yace shi bai sani ba amma kuma yadda turawa ke auna wasu abubuwa ba daidai suke da na Najeriya ba, idan kuma aka bi tasu mutum zai daina shan abubuwa da dama. Shi dai yace ba zai daina ba saidai idan bashi da kudi.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5