Wata Kafar Robot: Tafiya Kamar Jinjiri, Fahimta Ta Kare!

Wata sabuwar fasahar Kafa mai sarrafa kanta ga basira kamar ta jarirai da hazaka kamar Kare.

Kwararrun masu bincike daga Jami’ar California ta kudu, sun samo cigaba a kan Kafa ta mutum-mutumi mai sarrafa kanta, wadda zata iya koyan tafiya kamar jinjiri da fahinta kamar ta Kare.

Kafar dai mai na'ura zata iya koyar da tafiya a cikin minti biyar, da kuma gane wasu dabi'o'i. Duk wannan don ya taimaka ne ga mutane da suka rasa kafafuwansu.

Ta wani fannin kuma, Kafar zata iya koyan yadda zata bada taimako ga marasa kafiya, dake neman taimako da gajiya.

Masu binciken su ce nan da ‘yan shekaru kadan za a fara amfani da wannan kafar domin taimakawa ga mutane da kasa baki daya.