Blessing Bulsu tana cikin rukunin jami'an da aka dauka kan mukamin sifeto a hukumar ta shige da ficen baki.
Yayinda ake koyar dasu Blessing Bulus ta bujurewa umurnin malaminta na cewa ta koma aji inda sauran 'yanuwanta suke daukan darasi amma ta cigaba da zama waje. A lokacin da malaminta ya matsa mata lamba ya yi mata tsawa irin ta masu sanye da kayan sarki ta shiga aji sai ta wanke fuskarsa da mari.
Al'amarin ya ja hankalin ma'aikata da kuma bakin da suka ziyarci makarantar. Majiyoyi a kwalajin sun ce tun lokacin da Blessing Bulus ta isa kwalajin take yin abun da ta ga dama da kuma ranta yake so. Babu wanda ya isa ya ce mata uffon kawai saboda ta kasance tana auren shugaban hukumar shige da ficen baki ta Najeriya.
Kodayake jami'ar hulda da jama'a ta kwalajin Amina Aliyu ta ki cewa komi dangane da wannan batun domin linzami ya fi bakin kaza amma wasu 'yan Najeriya sun yi tsokaci akan lamarin.
Wani ya ce bisa gaskiya yakamata a kori Blessing Bulus daga makarantar. Yace shin saboda tana matar shugaban hukumar dalili ke nan da ba za'a hukumtata ba? Idan an tafi a hakan nan kasar ba zata cigaba ba.
Wani kuma cewa ya yi a duba dokar hukumar duk abun da ta fada a yi anfani da ita a kanta a hukumtata.
Farfasa Aliyu Dauda na fanin koyas da aikin malunta a jami'ar Bayero dake Kano ya yi bayanin dangantaka dake akwai tsakanin malamai da dalibansu. Dangantaka ce irin ta da da ubansa ko kuma 'ya da uwarta. Idan har aka wayi gari dalibi baya ganin kimar malami, shi kuma malami baya ganin shi uba ne ga dalibi to tafiya ta wargaje.
Amma Barrister Audu Bulama masanin shari'a da dokokin aiki na cewa tsarin aikin kayan sarki yana kyamar aure tsakanin ma'aikata guda biyu, musamman idan ya zanto daya babba ne daya karami dalili kuwa shi ne, hakan zai iya shafar tarbiya da da'a na aikin da suke yi. Koda kuma an yi auren doka ta tanadi cewa lallai auren nan ya zama iya a gida ne. Idan sun zo wurin aiki dole su yi kain da nain ba sani ba sabo. Yace idan Blesing Bulus ta cigaba da aiki a hukumar to badakalar da zata aiwatar bata da iyaka. Lallai dole ne makarantar ta dauki matakan korarta. Idan kuma mijinta ne ya daure mata gindi to shi ma a bincikeshi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5