Wasu Fulani makiyaya a jihar Filato sun bayyana bullar wata cuta da ta hallaka masu shanu da dama.
Makiyayan sun ce basu saba ganin irin cutar ba domin tana hallaka shanu cikin dan karamin lokaci.
Abdullahi Udoji ya shaida cewa a cikin kwanaki uku ya rasa shanu guda saba'in. Yana mai cewa shanun sun gamu da wani ciwon da shi bai gane kanasa ba. Yace da zara saniya ta kamu da ciwon bayanta zai zama tamkar ya kamu da wuta. Idan kuma an yi mata allura sai wuyanta ya kandare sai kuma mutuwa. Idan kuma saniya ta samu wuri mai danshi sai ta kwanta ta mutu.
Shi ma Saleh Gidado yace lamarin cutar dake hallaka shanun ya yi muni kwarai. Shi kansa ya rasa shanu sittin. Yace da suka kai wani kurmi sai shanun suka rikice har ya soma rasasu.
Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah reshen karamar hukumar Bassa Umar Bakari yace suna neman agaji daga gwamnati domin takaita hasarar dukiyarsu.
Baicin tashi hasarar shugaban na Miyetti Allah ya ce akwai wadanda suka rasa ishirin, hamsin, talatin da dai makamantansu. Mun dauki abun kamar wasa,inji shugaban amma da suka ga lamarin yayi tsamari sai suka yanke shawarar gaya wa duniya ta ji.
Fulanin sun yi kokarin bincike akan jinin shanu saidai sakamakon da aka basu bai gamshesu ba suna kira a yi cikakken bincike domin kada shanunsu su kare.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5