A Spain ko Andalusiya, wasu 'yan yankin Catalonia sun yi zanga zanga a Barcelona yau lahadi suna adawa da matsa lambar da gwamnatin yankin Catalonia take yi na neman ballewa daga sauran kasar.
"Watakil mun juma ba mu ce komi ba," kamar yadda daya daga cikin masu zanga-zangar ya gayawa kamfanin dillancin Labarai na Faransa.
Wannan zanga-zangar tana zuwa ne mako daya bayan da 'yan yankin suka kada kuri'a mai rinjaye na ayyana 'yancin cin gashin kansu. A kuri'ar raba gardamar wacce gwamnatin kasar a Madrid ta ayyana zaman wanda ya sabawa doka, kashi 90 cikin dari na wadanda suka kada kuri'a, sun goyi bayan ballewa daga kasar. Sai dai kasa da rabin 'yankin ne suka fito domin wannan zabe.
Kuri'ar neman jin ra'ayin jama' jiddin yana nuna cewa galibin 'yan yankin na Catalonia sun gwammace ci gaba da zama kasa daya maimakon ayyana 'yancin kai.
Wadanda suka shirya zanga-zangar ta yau lahadi suka ce taken ganganin na su shine, "Mu dawo da amfani da hankali.".