In ma kowa a Najeriya bai ji dadin dage gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya ba, to ban da ‘yan jam’iyyar APC a jihar Zamfara, musamman magoya bayan bangaren ‘yan takarar gwamnan jihar Abdul'aziz Yari.
Har ya zuwa daren jiya dai jam’iyyar ta APC a jihar bata san makomarta a zaben ba, sakamakon matsayar hukumar zabe na cewa jam’iyyar a jihar ba ta da ‘yan takara a zaben na bana, kuma bata bada wata sanarwar warware matsayar ba, kwatsam sai ga sanarwar dage zabe.
Sai dai a bangare daya, duk da yake ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar da suke ta murnar matsayar hukumar zaben basu ji dadin dage zaben ba, suna ganin ba wani tasiri da hakan zai haifar.
To ko wannan ka iya kasancewa dama ga jam’iyyar APC a jihar ta samun shigar ‘yan takarar a zaben? Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya ce yana fatan hakan.
Da tsakiyar dare ne dai hukumar zaben Nigeria ta bada sanarwar dage babban zaben kasar da mako daya, lamarin da ya sa al’amuran yau da kullum suka dawo tamkar yadda aka saba a babban birnin jihar.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5