Duk da tsaikon da aka samu da kuma wasu ‘yan matsaloli da aka fuskanta musamman da na’urar tantance katin zabe da ma kamala zabe a makare a wasu rumfuna a jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara, ‘yan siyasa da masu zabe sun bayyana gamsuwarsu da sabon tsarin gudanar da zabe.
Sanata Abdallah Wali dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, shi ma ya bayyana gamsuwarsa da sabon tsarin, abinda yace zai magance matsalar magudin zabe dake addabar tsarin zabe a Najeriya.
Ita ma jam’iyyar Adawa ta APC ta jinjinawa hukumar zaben Najeriya akan sabon tsarin. Sani Hukuma Zauro, babban jigo ne a jam’iyyar APC a jihar Kebbi shima ya yabawa shugaban hukumar zabe Alhaji Attahiru Jega saboda sabon tsarin.
Baki daya dai an gudanar zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisa salun alun a jihohin Sokoto Kebbi da Zamfara duk da cewa dai an ba’a fara zabe da wuri ba a wasu rumfunan.
Your browser doesn’t support HTML5