Wasu dubban yan jamhuriyar Nijar sun gudanar da gangamin a ranar Asabar a harabar majalissar dokokin kasaR dake birnin Yama,i da nufin matsa lamba ga sojojin Amurka su fice daga kasar, makwanni kusan 4 bayan da hukumomin kasar ta Nijar suka bada sanarwar yanke huldar aiyukan soja da Amurka.
Gangamin wanda ya sami halartar shugabanin majalissar soja ta CNSP shine na farko da aka shirya domin nuna kin jinin dakarun Amurka dake da sansani a yankin Agadez.
Shugabar kungiyar mata yan gwagwarmaya ta Nijar, Madam Fatima tace, sun fito gangamin ne domin nunama duniya irin karfin da yan kasar ke da shi, da kuma jaddada goyon bayan su ga jagororin mulkin sojin kasar bisa kudurin da suka dauka na umartar sojojin Amurka su fice daga kasar.
Ta kara da cewa, kamar yadda sojojin Faransa suka fice daga Nijar, lallai ne su ma sojojin Amurkan su hanzarta ficewa daga kasar, kuma yan kasar Nijar na goyon bayan wannan mataki na gwamnatin CNSP