'Yan Kunar Bakin Wake Sun Halaka Jami'an Tsaro A Syria

  • Ladan Ayawa

Hari bom din da aka kai da mota a Jos, Mayu 22, 2014.

Sakamakon wani hari da aka kai a Syria yayi dalilin mutiwar mutane 10 kana wasu da dama sun samu rauni

Sama da mutane 10 aka bada rahoto mutuwar su a wani harin kunar bakin wake da aka kai a caji ofis Damascuss babban birnin Syria. Kanfanin dillacin labarai na Faransa ya ambato maaikatar cikin gidan kasar tana cewa ‘yan kunar bakin wake su biyu ne suka tarwatsa kan su a caji ofishin dake unguwar da ake kira Al-Midan, wannan yayi dalilin mutuwar mutane da dama galibi farar hula da kuma wasu ‘yan sanda. Kamar yadda kungiyar dake rajin kare hakkin Bil’Adama a Syria mai cibiya a Ingila tace mutane 11 ne suka mutu sakamakon wannan harin kunar bakin wake, wadanda suka hada da ‘yan sanda. Sai dai ana samun rahotannin dake karo da juna da ke cewa wata mota ce tayi bindiga gaban wannan caji ofis din. Motocin daukar maras lafiya sun garzaya zuwa wurin, kuma hukumomi sun killace wurin. Ahalinda ake ciki kum,sakamakon hare haren da kungiyar ISIS ta kai kan mabiya darikar Shi’a a Afghanistan a lardunan kasan masu yawa, gwamnatin kasar ta dauki farar hula ‘yan shi’a aikin kare muhallan ibadar su. Masu aikin tsaron da yawansu ya kai 505 an basu makamai, kuma za’a rika biyansu albashin kimanin dala dari a wata, akmar yadda ma’aikatar cikin gidan kasar tayi bayani.