Jami'ai sun ce 'yan gudun hijira 19, ciki har da yara, sun mutu bayan da tirelar da ke dauke da su ta kauce daga hanya, har ta yi ta mirgina, sannan ta fado can kasa daga saman wata gada a yammacin Turkiyya.
Baya ga mace-macen, mutanen da su ka ji raunuka kuma sun kai 11 a wannan hatsarin, wanda ya auku yau Lahadi, a cewar hukumomi.
Gungun 'yan gudun hijirar na tafiya ne daga Aydin zuwa Izmir, a cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu, mallakin gwamnati. Nan take dai babu wani bayani kan kasashen da bakin hauren su ka fito.
Jiya Asabar ma, wasu 'yan gudun hijira 11 sun mutu a kasar Girka, bayan da motar da ke dauke da su ta yi karo da wata tirela. Bayanai na nanu cewa kwanan su ma wadan nan bakin hauren su ka ketara zuwa cikin Girka daga kasar Turkiyya, kuma sun nufi babban birnin nan na arewacin Girka ne wato Thessaloniki.