Wasu Yan Bindiga Sun Tuba A Adamawa

Shugabannin Miyatti Allah

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Adamawa CP Audu Madaki, ya bayar da lambar yabo ga shugabannin kungiyar miyetti Allah da ke taimakawa a yanzu wajen zakulo masu garkuwa da jama'a da ke boyewa a dazuka.

Kwamishinan ya yaba da hadin kan da 'yan Miyetti Allah ke badawa a yanzu da ta kai har wasu masu garkuwa da jama'a tuba su biyar, batun da ya ce rundunar 'yan sandan za ta cigaba da hada kai da kungiyoyin sakai don, kwalliya ta biya kudin sabulu.

Yanzu haka dai wannan matsalar ta garkuwa da jama'a na neman durkusar da harkokin kasuwanci a wasu sassan Najeriya, batun da Alhaji Ibrahim Muhammad da ke zama mataimakin shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta Najeriya mai kula da jihohin arewa 19, ke ganin dole a ta shi tsaye.

Alhaji Aliyu Alhaji Abare da ke zama shugaban kungiyar Miyetti Allah na shiyyar arewa maso gabas, shi ya wakilci shugaban kungiyar na Najeriya. Ya yi kira ga jama’ar Najeriya da su tashi tsaye a hada karfi da karfe domin ganin an magance matsalar tsaro a fadin Najeriya.

Saurari Cikakken Rahoton Ibrahim Abdulazeez Cikin Sauti

Your browser doesn’t support HTML5

ADAMAWA: Wasu Yan Bindiga Sun Tuba