Firai Ministan rikon kwarya Claude Joseph ya ce wasu 'yan bindiga sun kashe shugaban Haiti Jovenel Moïse.
WASHINGTON DC —
An kashe shugaban ne a cikin dare a wani hari da aka kai a gidan kansa ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa, Joseph ya ce wasu gungun mutane da ba a san ko su wanene ba ne ke da alhakin kisan, wanda ya kira "mummunan kiyayya, rashin mutunci da dabbanci."
Ya kuma ce matar Moïse, Martine, ta ji rauni kuma an kai ta asibiti don kulawa.
Haiti na fuskantar rikice rikicen siyasa da rarrabuwa gami da hauhawar rikice-rikicen ƙungiyoyin ta’adda.