Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba, sun kai hari a garin Gwaram inda suka farma wani banki da ofishin 'yan sanda, kana suka jefa bam a kan wata kotu.
WASHINGTON, DC —
Harin ya yi sanadiyar mutuwar 'yan sanda guda bakwai da masu gadi biyu.
Kakakin 'yan sandan jihar Jigawa DSP Abdul Jinjiri, ya tabbatar da kai harin kuma yayi karin haske. Banda wadanda aka kashe babu wanda ya ji rauni. Babu kuma alkaluma akan kudin da maharan suka sace a bankin.
Wani ganau ya bayyana yadda lamarin ya faru. Yace "kawai suna zaune sai suka ji harbe-harbe da kuma karar bam, an jefa bam a kotu da kuma ofishin 'yan sanda. Daga bisani suka fasa kofar banki suka shiga. Daga nan sun shiga wani gidan da aka kammala gininsa shi ma sun yi harbe-harbe sun kuma kone. A ofishin 'yan sanda aka rasa rayuka." Lokacin da shi ganau din ya je wurin ofishin 'yan sanda da kotu na cin wuta.
Wannan abun da ya faru ya saka an kara karfafa tsaro a garin Gwaram da kewaye duk da cewa su 'yan bindigan basu je ko ina ba illa wuraren da suka kai hari. Haka kuma basu taba kowa ba a garin.
DSP Abdul Jinjiri yace yanzu haka bincike yayi nisa domin gano wadanda suka kai harin. Mr. Jinjiri ya da cewa "dama can suna karfafa matakan tsaro akan iyakokin jihar ta Jigawa, sun kara tura jami'ansu a wasu kananan hukumomi dake makwaftaka da wasu jihohi."
Kawo yanzu dai hankalin jama'ar garin ya tashi yayin da wasu ke nufin barin garin. Mahukunta na kwantar musu da hankali kada su bar garin.
Ga rahoton Mahmud Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5