Wasu ‘Yan Bindiga Sun Fasa Wani Banki a Jihar Ondo Tare da Kashe ‘Yan Sanda Uku

Wasu 'yan bindiga barayi masu fashi da makami

A garin Ifon cikin jihar Ondo, wasu ‘yan fashi da makami sun fasa bankin Skye sun kwashe makudan kudi kana suka kashe ‘yan sanda uku yayinda suka yi bata kashi da jami’an tsaro

Jiya Alhamis ne wasu gungun ‘yan fashi da makami suka kai wa bankin Skye hari a garin Ifon cikin jihar Ondo.

‘Yan fashin sun kashe jami’an ‘yan sanda uku dake tsaron bankin kafin su fasa kofar bankin mai sulke, abun da ya basu damar kwashe makudan kudade.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Ondo, Femi Joseph, ya yiwa Muryar Amurka karin bayani ta wayar tarho.

A cewarsa dai wajejen karfe uku na rana ne, yayinda bankin ke gap da rufewa, ‘yan fashin suka iso bankin cikin motoci uku. Yace mutanen sun kai ishirin dauke da muggan makamai. Duk da cewa ‘yan sanda sun yi bata kashi da su amma saboda yawan barayin, sun sha karfin ‘yan sanda har suka kashe uku daga cikinsu.

Dangane da matakin da ‘yan sanda suka dauka yanzu, Femi Johnson ya ce tuni suka bi sawunsu don cafkesu domin su fuskanci fushin shari’a bisa laifin da suka aikata.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Fasa Wani Banki a Jihar Ondo Tare da Kashe ‘Yan Sanda Uku - 2' 38"