Tsarin tsamo shanun da ake sacewa a Najeriya wanda wasu kwararru da hadin kan wani kamfanin sadarwa a Najeriya na nufin ganin koda an sace saniya to ba zata yiwu a sayar da ita ba saboda akwai yadda za'a gano mai ita.
Alhaji Ibrahim Maigari Ahmadu shi ne shugaban kamfanin kwararrun da suka fito da sabuwar hikima tare da hadin gwuiwar wani kamfanin sadarwa.
A taron jihohin arewa 19 na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Kaduna Alhaji Ahmadu ya yiwa manema labaru karin haske dangane da shirin.
Yace sama da shekaru biyu ko ukku suka dinga tunanen yadda zasu sami hanya mafi sauki su magance matsalar sace-sacen shanu. 'Yar naurar da ake sawa jikin dabbar zata nuna lamabar mai ita.
Alhaji Lawal Batagarawa ya bada jawabin wayarda kawunan Fulani akan yadda za'a dakatar da sace sacen shanu a Najeriya kuma ya gargedsu da su rungumi sabon shirin.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5