Wasu Shugabannin Kungiyar Maharban Najeriya Sun Bukaci Kowane Maharbin Arewa Maso Gabas Ya Biya N12,000 Kudin Horaswa

Shugabannin Maharban Jihar Adamawa

Yanzu haka wata badakala ta kunno kai a kungiyar yan sa-kai ta maharban Najeriya inda aka samu wasu shugabannin kungiyar ke tatsar ‘ya’yan kungiyar ta hanyar karbar kudade na naira N12,000 daga ko wane maharbi da sunan kudin horaswa, batun da wasu maharba ke kokawa akansa

‘Yan sa-kai na maharba na taka muhimmiyar rawa a yakin da ake da ‘yan Boko Haram, musamman a jihohin arewa maso gabashin Naijeria.

‘Ya’yan kungiyar maharban reshen jihohin arewa maso gabas dake taimakawa jami’an tsaro a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram sun koka da amsar kudi a wajensu na naira dubu goma sha bibbiyu daga ko wani mutum, da sunan za’a basu horo a karkashin kungiyar.

‘Ya’yan kungiyar dai na zargin cewa wasu shugabanin kungiyar yanzu haka suna bin jihohi suna tatsar su, abun da suka ce basu san da shi ba a tarihin kungiyar maharba.

Abubakar Bauchi da Yakubu Shelleng, wadanda ke cikin ‘ya’yan kungiyar dake cikin masu korafin, sun ce basu amince ba.

Shima a martaninsa, Mr Philip Japhet Ngurore, sakatarengudanarwar kungiyar maharban a Najeriya, ya musanta zargin cewa da yawunsu ake karbar wadannan kudade.

Kawo yanzu dai duk kokarin ji daga bakin shugaban kungiyar maharba na shiyar arewa maso gabas, Alhaji Muhammad Usman Tola, ya ci tura ko da yake wata majiya ta bayyana cewa wannan batun samun horo na da nasaba da sabanin dake akwai a tsakanin wasu shugabanin kungiyar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Kungiya Ta Bukaci Kowane Maharbin Arewa Maso Gabashin Najeriya Ya Biya N12000 Kudin Horaswa - 3' 33"