Shugabannin kabilar Igbo sun yi taro a garin Asaba babban birnin jihar Delta da kuma wani taron da suka yi a Enugu babban birnin jihar Enugu inda suka nisanta kansu da batun ballewar yankinsu daga Najeriya.
Wata da ta furta albarkacin bakinta tace maimakon ana kai da kawowa ana tada hankulan mutane kamata yayi a zauna lafiya da juna ba a cigaba da fafutikar kafa kasar Biafra ba.
To amma wani cewa yayi shi bai goyi bayan a zauna tare ba. Duk 'yan kabilar Igbo dake arewacin Najeriya su dawo kasarsu 'yan arewacin kasar kuma dake kasar Igbo su koma arewa. A cewarsa taron na banza ne domin ba'a gayyaci jagoransu ba, Nnamdi Kanu. Yace su Biafra suke goyon baya.
Wata tace kamata yayi a yi addu'a a cigaba da zama 'yan Najeriya, 'yan kasa daya ba tare da rabuwa ba.
To amma a taron shugabannin kabilar ta Igbo sun yi watsi da kafa kasar Biafra sai dai sun bukaci a sake sabon fasalin tsarin kasar.
Kungiyoyi irinsu Ohaneze N'digbo sun amince da zaman lafiya. Onarebul Faisal Lawal mai ba gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha shawara kan baki dake zaune a jihar ya bayyana fahimtarsa. Yana mai cewa taron yana da kyau saboda can baya ana ganin maganar bata damu gwamnonin ba to amma yanzu sun yi magana.
Alhaji Bafarawa tsohon gwamnan Sokoto na jam'iyyar adawa ta PDP yace duk kiraye-kirayen a raba kasa rashin adalci ne ya haddasasu. Yana mai cewa gwamnatin yanzu ba ita ce ta fara mulkin kasar ba amma da shigowarta aka fara kiran a raba kasar.
A saurari rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5