Wasu Mutune Dake Sarrafa Shinkafar Waje A Matsayin Ta Gida Sun Shiga Hannu A Jihar Adamawa

Jami’an hukumar kwastam a jihar Adamawa sun cafke wata motar wake amma shinkafar waje ke cikinta da aka shigo da ita daga kasar Kamaru.

A daidai lokacin da ake ci gaba da tsokaci game da rufe iyakokin Najeriya, jami’an hukumar kwastam a jihar Adamawa sun sami nasarar gano wani wuri da ake sanya shinkafar waje a buhuhuna a matsayin shinkafar gida domin shigar da ita kasuwanni.

Gano wurin ya biyo bayan wani samame da jami’an hukumar suka kai inda suka cafke mutune 15 yayin da suke gudanar da wannan aikin.

A lokacin da ya jagoranci wata tawagar 'yan jaridu zuwa wajen da ake wannan aika-aikar, kwanturolan hukumar kwastam mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, Mr Kamardeen Olumoh yace sun cafke buhunan shinkafar waje guda 900 da kudin fiton su ya kai naira miliyan 14 da dubu dari biyar ( N14.5 million).

Bayan haka, jami’an hukumar sun sake cafke wata mota dake dauke da wake, alhali shinkafar waje ce aka lullube da aka shigo da ita daga kasar Kamaru.

Tuni dai hukumar ta tura gargadi ga 'yan kasuwa akan cewa cikin kwanakin nan zata kai samame kasuwanni domin bankado kayayyakin waje, a cewar Mr. Kamardeen Olumoh.

To ko yaya al’umma ke kallon matakan da ake dauka a yanzu? Mallam Uba Yakubu, wani mai goyon bayan gwamnatin Buhari ne, yace wannan mataki yayi daidai.

Hukumar da ke yaki da fasa -kwabri a Najeriya wato kwastam, ta ce za a ci gaba da rufe kan iyokokin kasar da ke tudu har zuwa lokacin da Najeriya ta sami cikakken hadin kai daga sauran kasashen da take makwabtaka da su.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Mutune Dake Sarrafa Shinkafar Waje A Matsayin Ta Gida Sun Shiga Hannu A Jihar Adamawa