Daruruwan mutanen kauyen Kamali a karamar hukumar Michika dake kan iyaka da kasar Kamaru sun koka da mawuyacin halin da suke ciki.
Mutanen sun kwashe kimanin makonni biyu suna kan tsauni inda babu abinci ko katifun kwaciya.
Wadanda alamarin ya shafa sun ce suna ta gudu suna sauka daga kan dutse domin babu inda zasu duk a kokarin tsira da rayukansu sabili da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram. Sun roki a yi masu hanya su koma garinsu.
Abun da ya fi damun mutanen shi ne yadda 'yan Boko Harama suna bi suna karkashesu kamar kiyashi. Yanzu dai akwai 'yan Najeriya masu dimbin yawa da suka makale tsakanin kasar da kasar Kamaru.
Mr Emmanuel Kwaja wani tsohon dan jarida kuma shugaban wata al'ummar yankin yayi karin bayani. Yace mutanen da suka makale a tsaunuka basu da abinci kuma babu yadda za'a kai masu abinci. Kowa na tsoron zuwa wurin sabili da 'yan Boko Haram wadanda yanzu sun kame kusan duk kauyukan dake makwaftaka ta wurin. Duk wata hanyar shiga wurin da mutanen suka makale sun datse.
Shugaban yankin Mr Kwaja ya kira shugaban kasa da babbar murya ya aika da sojoji da dama domin a fatattaki 'yan Boko Haram din. Ya bukaci a yi anfani da jirgi mai tashin angulu ya soma saukar ma mutanen abinci.
Amma sojoji na gadin gidan babban hafsan hafsoshin Najeriya Janaral Alex Badeh dake cikin garin Michika. Wai sojojin sun tsaya gidan Janaral Badeh ne kawai.
Saidai hukumomin Najeriya sun ce suna sane da mutanen dake kan tsaunukan kuma ana kokarin kai masu tallafi. Hukumar bada tallafin gaggawa tace tana shirya kayan da zata kai masu tare da wasu 'yan kasar dake gudun hijira a wasu sassa har da cikin Kamaru.
Alhaji Muhammed Kanar babban jami'in hukumar bada tallafin gaggawa mai kula da arewacin Najeriya yace sun tura mutane domin a samar masu hanyar da zasu bi su kai doki da kuma neman rakiyar jami'an tsaro. Yace sun riga sun tanadi kayan da zasu kai.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5