Yan sandan Ashakayankin Ndokwa a jihar Delta sun samu nasarar kama wasu matasa shida ‘yan kungiyar asiri wadanda suka yiwa yara mata fyade a matsayin wata hanya na shiga kungiyar.
Matasan wadanda shekarunsu ke tsakani goma sha shida zuwa ashirin sun tsere ne a lokacin da suka ga ‘yan Sandan amma an cafke daga bisani lokacin da wani wanda ake zargi da aikata laifin tare dasu yayi wa ‘yan Sanda bayani.
A cewar kwamishinan ‘yan Sandan jihar Delta Mr. Zanna Ibrahim, yace cafke su ya biyo baya wani tsegumi ne da suka samu inda suka je wani Otel inda ‘yan kungiyar asirin suke.
Ya kara da cewa wanda ake zargin suna ganin ‘yan Sanda sai suka gudu, tare da haura katangar Otel din a garin hakan ne suka bar babur daya a wajen mai lamba UWN852 QR Enugu, takalama guda shida, wayoyi hannu samfarin Nokia guda biyu, samfarin Tekno daya da kuma Gionee daya.
Yace duk da haka wata mace a cikin ‘yan kungiyar bata tsira ba inda ‘Yan Sanda suka kamata, ta kuma yi musu bayani cewa anyi mata fyade da zummar shigar da ita cikin kungiyar mai suna Vikings Queen.
Kwamishinan na ‘yan Sanda yace bayanin wacce aka sa aka kama mutum biyar daga cikinsu duk ‘yan garin Ashaka ne
Ya kuma kara da cewa sun amsa laifinsu na zama ‘yan kungiyar asiri mai suna Junior Vikings Confraternity. Duk da haka, ‘yan Sanda na ci gaba da binciken lamarin.