Tubabbun mutanen, wadanda ba a bayyana sunayensu ba sun kuma ba da hadin kai kan cewa za su taimaka wajen magance wannan matsala ta garkuwa da mutane da ta zama ruwan dare a yankin.
Daya daga cikinsu ya sheda wa wakilin VOA Ibrahim Abdulaziz cewa, “muna kama mutane ne don mu samu kudi, kuma yadda muke samun kudin a banza haka kudin ke karewa a banza.”
Ya kuma yi kashedi ga tsoffin abokanan huldar tasa.
“Duk mutanen da suka san suna aikin garkuwa da mutane har yanzu, wadanda na yi aiki da su a baya, idan ba su kawo kansu ba, to ni zan mika su ga hukuma,” a cewarsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Audu Madaki, ya ce a yanzu suna samun ci gaba sosai wajen gudanar da ayyukansu.
Ya kara da cewa, suna kai samame cikin yankunan da masu garkuwa da mutanen ke boye wa domin hana su zama a yankunan.
“Ta hakan muke samun hana su gudanar da wadannan miyagun ayyukan, lamarin da ke janyo su kawo kansu wurinmu domin mu taimaka masu da sana’o’in da za su iya yi,” inji kwamishinan.
Ya kara da cewa, “mun kafa masu sansanonin da za su dinga aiki da ‘yan kungiyar Miyetti Allah, sannan muna karbar bayanai na tsoffin abokan aikinsu masu garkuwa da mutane domin mu kama su.”
A lokuta da dama, akan zargi al’umar Fulani da hannu dumu-dumu a harkar satar mutane a sassan Najeriya.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah Alhaji Ja'oji Isa a jihar ta Adamawa, ya ce za su ci gaba da ba da hadin kai domin a kawo zaman lafiya a jihar.
Wannan nasarar ta biyo bayan kiran da manyan sarakunan jihar suka yi tare da hadin gwiwar kungiyoyin Fulani irinsu Miyetti Allah, na cewa, za'a gudanar da addu'o’in tsinuwa wato Puulaku, ga duk wani bafillace da ke da hannu a ayyukan garkuwa da jama'a.
Hakan duk na faruwa ne kwanaki kadan bayan da aka gudanar da adu’o’in zaman lafiya a jihar, bisa matsalar tsaro da ake yawan fuskanta.
Saurari cikakken rahoton daga bakin wakilinmu Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5