Manoman su goma sha daya aka yi masu kisan gilla ne akan hanyarsu ta zuwa share gona kusa da birnin Maidugurin jihar Borno.
Yawaitar hare-haren 'yan Boko Haram din a kewaye da kuma cikin Maiduguri ya sa ayar tambaya a zukatan mutane game da ikirarin karya lagon kungiyar 'yan ta'addan da sojojin Najeriya suke yi.
Su dai mutanen da suka gamu da ajalinsu kamesu aka yi kana aka yankasu gunduwa gunduwa a wani kauye da ake kira Amarawa dake karamar hukumar Kondiga a jihar Borno mai tazarar kilomita 16 da birnin Maiduguri.
Shaidun gani da idanu sun shaidawa manema labarai cewa maharan sun zo ne akan babura kana suka farma mutanen yayinda suka kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu.
Tun da dadewa mazauna wuraren sun sha fadawa jami'an tsaro alamuran dake faruwa a yankinsu musamman yawan hare-haren da suke fuskanta saboda basu da nisa da babban birnin Maiduguri.
Wani mazauni a kauyen ya kara bada labarin yadda 'yan Boko Haram din suka dinga zuwa cikin kauyukan dake kewayensu suna kashe mutane uku ko hudu tare da jefa gawarwakinsu cikin rijiyoyi. A cewarsa wajen wata daya ke nan suna fama da hare-hare saboda babu jami'an tsaro kusa dasu.
Ga rahotn Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5