Wasu Mahara Sun Kai Hari Yankin Shiroro Jihar Neja

Fulani Makiyaya

Wasu mahara da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a kauyen Erana ranar kasuwar garin inda suka shiga harbin mutane.

Maharan dake kan babura wajen su arba'in dauke da bindigogi sun kai hari a Erana dake cikin karamar hukumar Shiroro yayin da kasuwar garin ke tsakiyar ci.

Harin ya faru ne ranar Larabar da ta gabata da misalin karfe uku na rana. Ganao sun ce maharan sun share awa biyu da rabi suna kai hari kan Fulanin da suka gani a cikin kasuwar.

Kodayake babu labarin mutuwa amma mutane da dama sun jikata kana an yi asarar dukiyoyi masu dimbin yawa. Alhaji Jibril Usman Erana shugaban al'umman yankin yace mutanen akan babura ashirin kowanne dauke da mutum biyu biyu suka shiga kasuwa suna ta harbi da bindigogi. Sun sassari mutane da adduna suna neman Fulani. Sun jima Fulanin da suka samu munanan raunuka.

Tuni kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar Neja ta nuna damuwa akan harin da aka kaiwa 'ya'yanta.Alhaji Abubakar Sadiq sakataren kungiyar reshen Neja yace hukumomin tsaro sun nuna masu suna bincike domin gano wadanda suke da hannu a harin.

Rundunar 'yansandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma tace tana bincike.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Mahara Sun Kai Hari a Yankin Shiroro Jihar Neja - 2' 56"