Wata kungiyar kasar Saudi Arabiya dake bada tallafi ga marasa karfi a Najeriya da ake kira International Islamic Relief Organization tare da hadin gwuiwar wata kungiyar likitoci mai suna Smile Healthcare Foundation suna tallafawa mutanen dake da matsalar ciwon ido a jihar Borno.
Kungiyoyin na gudanar da aikin ne kyauta..
Muryar Amurka ta zagaya asibitin idanu inda kungiyoyin ke yiwa mutane aiki. Ta samu ta zanta da wasu da suka ci moriyar wannan taimako.
Wadanda aka zanta dasu sun fito ne daga sassa daba daban na jihar Bornon. Sun bayyana jin dadinsu da ayyukan da aka yi masu.
Dr Abba Saleh jagoran kungiyar Smile Healthcare Foundation, yace suna duba mutanen dake zuwa wurinsu idan akwai wadanda za’a yi masu aiki sai su yi. Wadanda kuma na bada magani ne sai su basu. Akwai kuma wadanda kuma tabarau, suke bukata kuma ana basu domin su gani sosai.
A cewar Dr Saleh suna zaton zasu duba kimanin mutane dubu biyar, to amma har sun duba fiye da mutane dubu goma, kuma mutane sai kara zuwa su keyi, saboda haka zasu ci gaba da aikin.
Baicin taimakon da suke samu daga kungiyar International Islamic Foundation ta Saudiya wadda take bada kashi 75, attajirai da masu jin kai cikin kasar suna taimaka masu da kashi 25 daga cikin dari. A saboda haka suna yiwa mutane aiki ko basu magani ba tare da karban ko kwandala ba.
Kawo yanzu kungiyoyin sun kashe sama da Nera miliyan biyar akan ayyukan da suke yi kuma suna zaton bisa ga abubuwan da zasu yi zasu kashe kimanin Nera miliyan 20.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5