Biyu daga cikin manyan kungiyoyi masu hamaiya a Syria, National Council da kuma National Coordinating Body for Democratic Change sun hada kai domin shata taswirar kafa mulkin Democradya idan har Allah yasa aka hambarar da gwamnatin shugaba Bashar Al Assad.
Jiya juma’a da dare wakilan wadannan kungiyoyi suka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a birnin Alkahira data tanadin yadda za’a kafa mulkin democradiya idan masu zanga zangar kin jinin manufofin gwamnati suka samu nasarar hambatar da gwamnatin Assad.
An kula wannan yarjejeniyar ce, a yayinda ake ci gaba da yin rikici a Syria duk da kasancewar masu lura na kungiyar kasashen Larabawa wadanda ke nazarin yadda gwamnati take maida martini akan masu zanga zangar.
Masu gwagwarmaya sunce a jiya juma’a sojoji Syria sun kashe akalla mutane talatin da biyu.
Wani kwamitin masu hamaiya yace an kashe yawancin mutanen ne a lokacinda sojojin gwamnati suka bude wuta akan masu zanga zangar ki jinin gwamnati a wurare da dama.