Don haka ne suka bukaci gwamnatoci da hukumomin ketare, irin su Amurka da Burtaniya su dauki matakan da suka dace wajen hulda da gwamnan.
A cikin wata sanarwa da suka fitar a Kano, wakilan kungiyoyin da suka hada da Guardian Center for Development da amnesty international da kuma action Justice sun zargi gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da rashin mutunta umarnin kotu da katsalanda akan ayyuakan majalisar dokoki dana bangaren shari’a.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Comrade Ibrahim Sulaiman daga kungiyar Amnesty, ta bada misali da yadda gwamnan ya ki biyan mawallafin Jaridar Daily Nigerian wato Jafar jafar wanda kotu ta umarci gwamnan ya biya wasu kudade biyo bayan janye karar da gwamnan ya kai shi jafar din a kotu.
Sai dai gwamnan na Kano ta bakin kwamishinan labaru Comrade Mohammed Garba ya musanta abin da kungiyoyin ke fadi yana mai bayyana lamarin a matsayin siyasa kawai.
Zargin taken ka’idojin demokaradiyya, da na rashin mutunta umarnin kotu da kuma katsalanda a bangaren shari’a dana majalisar dokoki ya dade yana yawo akan gwamnonin Najeriya, lamarin da ya kara kaimin fafutikar nemawa bangarorin biyu ‘yanci daga hannun gwamnonin.
Saurari cikakken rahoton a cikin a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5