Kansiloli 226 A Jihar Adamawa Sun Koka Da Rashin Biyansu Hakkinsu

Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Su dai kansilolin 226, sun yi cicirindo ne a ofishin mataimakin Gwamnan jihar inda anan ne suka gana da Gwamnan jihar Adamawan Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, domin mika kukansu game da halin da suke ciki ayanzu.

Baya dai ga batun alawus na kujeru da ba’a basu ba tun hawarsu karaga,haka nan kuma sun nuna bacin ransu game da shakulatin bangaro da suke zargin ana nuna musu a jihar, lamarin da ya kai ga rage wa’adin su da kuma ma rufe karamar hukumar Yola ta Arewa na kusan fiye da shekara guda, Hon Danjuma Hamman Adama Nbaleri, shi yayi jawabi ga Gwamnan a madadin kansilolin, inda yace yanzu haka suna cikin mawuyacin hali.

To sai dai kuma Gwamnan jihar Bindow Jibrilla, yayi musu alkawarin cewa da zara ya samu kudi, zai neme su takanas ya biya su.

Koma da menene dai yanzu lokaci ne ke iya tabbatar da ko shin zasu samu kudadensu kafin nan da karshen wa’adinsu dake karewa a watanni uku masu zuwa ko kuma a’a,yanzu an zura ido a gani.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaaziz da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Kansilolo 226 A Jihar Adamaw Sun Koka Da Rashin Biyansu Hakkinsu - 3' 02"