Wasu Kananan Hukumomin Kaduna Sun Kawo Sakamakon Su

Wani ma'aikacin zabe a Kano

Har ya zuwa cikin daren jiya Lahadi, hukumar zabe bata kammala tattara sakamakon zaben da aka gudanar na shugaban kasa da ‘yan majalisun dokokin tarayyar Najeriya na ranar asabar.

Domin kuwa har zuwa karfe daya saura na daren jiya Lahadi, kananan hukumomi goma sha daya ne hukumar zaben kawai hukumar zaben ta samu karbar sakamakon su daga wakilanta na kananan hukumomi.

Kananan hukumomin da suka kawo sakamakon su sun hada da Jaba, Kaura, Kajuru, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, sauran kananan hukumomin sun hada da Kudan, Kubau, Makarfi, Sanga. Dakuma kananan hukumomin Sabon Gari da Soba.

Jim kadan bayan karbar sakamakon kananan hukumomi goma sha daya cikin ashirin da ukun jihar Kadunan, jami’an dake gudanar da wannan aiki sukace a tafi hutu, saboda ganin babu daya daga cikin wakilan kananan hukumomi goma sha biyun da ake jira ya riga ya kawo nashi sakamakon, yayinda wasu kananan hukumomi dake da nisa daga birnin Kadunan, suka sanar ba zasu sami damar zuwa ba sai safiyar yau litinin.

Idan har komai ya tafi kamar yadda aka tsara to yau Litinin za’a sanar da sakamakon zaben a jihar Kaduna.