Joli Oka Donli daraktar hukumar hana safarar mutane ta Najeriya tace ta samu labarin kamfanoni na safarar mutane zuwa Saudiya da wasu kasashen Larabawa kuma tace ta tura rahoton wa bangaren dake sa ido da binciken lamarin.
Inji Joli Donli ana gudanar da bincike akan batun saboda haka tace ba zata yi magana a kai ba sai an kammala binciken. Amma ta jawo hankalin jama'a cewa su a hukumance basu ba kowa iznin yayi safarar 'ya'yan mutane zuwa kowace kasa ko kasashen Larabawa ba.
Wani likitan asibiti dake Abuja da suke tantance lafiyar wadanda ake safarar zuwa kasashen Larabawa yace abun akwai ban tsoro. Yace ana kawo yaran cikin motoci cike makil, maza da mata.Yanzu ma kusan gaba daya mata ake debowa a kawosu domin tantance lafiyarsu.
Inji ma'aikacin asibiti akwai wata ma da bata wuce shekaru 20 da haihuwa ba da tazo a tantanceta. Da aka yi mata tambaya sai tace tana da aure har da yaro daya. Tace da sanin mijinta ta baro dan domin shi mijin ma yana shirin tafiya kasar Larabawan.
Abdulahi Musa wanda yayi aniyar tafiya a da amma yanzu yace ya fasa. Yana mai cewa da farko akwai kamfanoni da suke neman mutane domin su kaisu Saudiya ta basu aiki. Yace sun yi masa alkawarin kaishi da matarsa saboda haka ya nema masu fasfo. Amma daga baya sai aka ce masa mata ne zasu fara tafiya sai yace idan ba zai tafi da matarsa ba ya fasa.
Wani Haliru Musa da tuni iyalinsa suke kasar Larabawa suna aiki shi ma yana jira ya tafi yana mai cewa a Najeriya babu irin wahalar da basu sha ba.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5