Hukumar zaben Jihar Neja a Najeriya ta ce an sami nasarar kubutar da ma’aikatan ta na wucin gadi daga wasu da ake zaton barayi masu garkuwa da mutane ne da suka so yin awon gaba da su a jihar a lokacin aikin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissu.
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne a yankin Kundu, dake karamar hukumar Rafi a lokacin da jami’an hukumar zaben suka je aikin zabe, al’amarin da ya haddasa rashin gudanar da zabe a rumfuna guda biyu dake wannan yankin, a cewar kwamishinan zaben jihar Neja, Farfesa Samuel Ogu, a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani.
Malam Ibrahim Abare, shi ne jami’in yada labaran hukumar zaben jihar ya ce, matsalar tsaron da aka samu a yankin ta shafi aikin da ya kamata su yi amma yanzu dai suna jiran hukuncin da babban Ofishin su na Abuja zai yanke. Ya kuma tabbatar da cewa akwatunan da aka sace babu komai a cikin su kuma an kwato su. Haka kuma yinkurin sace jami’an bai yi nasara ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Sabo, ya ce sun tarwatsa wani shirin hana yin zabe a wasu wurare da wasu bata gari suka so yi a kananan hukumomin Magama da Lapai, ya kuma ce sun sami nasarar damke wani mutum daya da ya sungumi akwatin zabe a garin Kuchi dake yankin karamar hukumar Lapai.
Ya zuwa yanzu dai hukumar zaben jihar Neja ta ce jam’iyyar APC ce ta lashe zaben ‘yan majalissar dattawa guda 3. Amma shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, barista Tanko Beji, ya ce har yanzu ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
Wannan dai na zuwa ne a yayinda hukumar zaben kasa ke tattara alkaluman da aka bata na sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalissa.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5