Wasu Jam'iyyu Sun Kalubalanci Rusa Su Da INEC Ta Yi

Bayan rusa jam'iyyun da hukumar za6e ta yi, Jam'iyyar ACD ta jagoranci wasu jam'iyyu 2 suka shigar da kara a kotun tarayyya inda suka nemi kotu ta dakatar da rusa jam'iyun, bisa dalilin rashin yi masu adalci, tunda ba a tuntu6e su kafin rusa jam'iyun.

Shugaban Jam'iyyar ACD Alhaji Musa Adamu Takai ya ce hukumar za6e ba ta ba su kudi domin tafiyar da jam'iyyun su ba, kuma duk sharrudan da hukumar za6e ta shimfida wa jam'iyyun, sun bi. Saboda haka Takai, ya yi zargin cewa son zuciya ya sa hukumar za6e rusa jam'iyyu ba bin doka ba.

Amma shugaban Jam'iyyar ACCORD kuma wanda ya ta6a rike kungiyar kula da Jam'iyyu ta kasa Mohammed Umar Nalado, ya ce shi yana goyon bayan matakin da hukumar zabe ta dauka.

Ya ce daukar wannan matakin yana kan dokar kasa balle ma an ta6a yi a baya amma ba a samu gallaba ba, saboda a lokacin babu dokar da ta ba hukumar za6e hurumi, a yanzu kuwa akwai doka.

Shi ma kwararre a fanin kimiyar shari'a Barista Mainasar Umar, ya ce doka ce ta ba hukumar za6e hurumin daukan matakin rusa jam'iyyun da ba su ta6uka komi a zabukan kasar ba.

Daga dukan alamu hukumar za6e za ta daukaka kara kamar yadda mai magana da yawun ta Aliyu Bello ya ce, su dokar kasa suka bi wajen rusa jam'iyyun.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kare tsakanin jam'iyyun da kuma dokar da kundin tsarin mulkin kasa ta tanadar.

A saurari rahoton Madina Dauda cikin sauti, daga Abuja, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Jam'iyyu Sun Kalubalanci Rusa Su Da INEC Ta Yi