Wasu Daga Cikin Masu Zanga Zanga A Hong Kong Sun Tsere Ma 'Yansanda

Dalibai kasa da 200 sun kasance a tsare a cikin wani shinge a Jami'ar Hong Kong, wacce ‘yan sanda suka zagaye ta tun ranar Lahadin da ta gabata.

Dinbin dalibai sun yi ta maza a yinkurinsu na tserewa, inda su ka ketare layin da 'yan sanda su ka shata, yayin da wasu kasa da 200 daga cikinsu, su ke cigaba da kasancewa a tsare a cikin wani shinge a Jami'ar Hong Kong, wacce ‘yan sanda suka zagaye ta tun ranar Lahadin da ta gabata.

Wakiliyar Sashin Sinanci na Muryar Amurka, Iris Tong, wadda ta kasance da daliban a Jami'ar ta Hong Kong, ta bayyana yanayin kunci da ake cikin a wurin, inda akalla matasa biyu su ka yi barazanar kashe kansu.

"Na ga wani yaro (ya na barazanar) daba ma wuyarsa wuƙa," in ji Tong. Ta kara da cewa, "Ban ga wani jini a wuyarsa ba, kawai ya yi magana ne game da yadda yake so ya kashe kansa. Amma wasu mutane sun ce ba lallai ba ne ya yi hakan, kuma sun gaya masa ya ajiye wukar."