Wasu Bakin Fulani Sun Kai Farmaki A Jihar Gombe

Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara

A Najeriya a jihar Gombe dake Arewa maso gabashin kasar an samu rahoton bullowar Udawa makiyaya dakan shiga gonakin manoma su barnata musu kayan amfanin gona da basu gama nuna ba kafin a kwaso uwa gida.

Udawan sun bullo ne a kananan hukumomin Akko da kuma Yamaltu Deba.

Shaidun gani da ido sun ce Udawan sun yi aika-aika a kauyuka sama da goma, inda bayan lalata amfanin gona, sun yi wa mata da dama fyade da kuma kwace wa manoman kudade da wayoyin salula, a cewar Muhammed Sani, wani ganau daga yankin.

Kwamishinan Tsaro na cikin gida a jihar Gombe Maji Dauda Batari ya tabbatar aukuwar lamarin a hukumance, in da ya ce tuni suka ziyarci kauyukan domin ganewa idon su abin da ya wakana.

Ya ce sun tattauna da Fulani makiyaya na cikin gida domin samo hanyoyin gano daga inda makiyayan suka fito domin daukar matakin da ya dace.

Wani tsohon shugaban karamar hukumar Yamaltu Deba da ya taba fuskantar bala’in Udawan a lokacin da ya ke mulki, ya shawarci gwamnatin jihar Gombe da ta hanzarta daukan mataki da kawo zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a yankunan da Udawan ke tu’annati.

Ga karin bayani daga Abdulwahab Muhammad

Your browser doesn’t support HTML5

Udawan Fulani sun kai farmaki a Gombe