Wasan Kwallon Kafa ne Kawai Yake Hada Kawunan 'Yan Najeriya - Gwamnan Kwara

'Yan wasan kwallon kafa na Najeriya

Duk 'yan Najeriya kawunansu rarraba suke saidai lokacin da kasar ke wasan kwallon kafa da wata kasa-inji gwamnan jihar Kwara

Gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed yace kwallon kafa ne kadai yake hada kawunan 'yan Najeriya yayin da kasar ke karawa da wata kasa.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar Alhaji Isiyaka Isa Gold ya wakilta a wani taron lakca da kungiyar 'yan jarida ta jihar Oyo ta shirya a Ibadan wurin bikin tunawa da cikar kasar shekaru 55 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka.

Gwamnan yace idan ba lokacin wasan kwallon kafa ba da Najeriya zata buga da wata kasa bai ga lokacin da 'yan Najeriya zasu zama daya ba. Yace da wuya a samu lokacin da 'yan Najeriya zasu zama tsintsiya madaurinkin daya ko kuma su yi tunanen kasarsu ce.

Da ya cigaba gwamna Ahned yace akwai wani shugaban Najeriya da kasar ta taba yi da ya ba yankinsa fifiko a lokacin da yake kan mulki fiye da kowane bangaren kasar. Yace to amma idan kasar na wasa da wata kasa a lokacin babu wanda zai ce shi Ibo ne ko Bahaushe ko Bayerabe ne. Kowa na kokarin cewa a samu nasara.

A cewar gwamnan halayen nuna banbanci ko na kabilanci ko na addini da bangaranci ba zasu taimaki kasar ta cigaba ba. Saboda haka ya bukaci 'yan kasar da su hada kawunansu ba tare da yin la'akari da wani banbanci ba. Hadin kawunan 'yan kasar ne kawai zai kaiga dorewar kasa da tabbatar da zaman lafiya da lumana.

Daga karshe kungiyar 'yan jarida ta jihar Oyo ta karrama gwamna Ahmed.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal..

Your browser doesn’t support HTML5

Wasan Kwallon Kafa ne Kawai Yake Hada Kawunan 'Yan Najeriya - Gwamnan Kwara