Wanne Irin Hukunci Ya Dace A Zartar Kan Masu Satar Fina-Finai A Najeriya?

Hukumar tantace fina finai ta Najeriya, ta damke wasu matasa uku, masu yin kan Ungulu da Zabo, da fina finan jaruman Najeriya. wanne irin hukunci ya kamaci irin wadannan matasa dake yiwa fina finan Najeriya zagon kasa domin zamewa darasi ga sauran matasa masu irin wannan tunani?

Muna bukatar sakonnin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.

Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com